Boris Johnson ya kwantanta matan masu sanya kallabin da su ke rufe fuskarsu da shi, Burkaa da cewa; sun yi kama da masu fashi da makami a cikin Banki.
Shi ma Alistair Burt da shi ne babban jami'i mai kula da harkokin Afirka da gabas ta tsakiya a ma'aikatar harkokin wajen Birtaniy, ya ce furucin na Johnson cin zarafi ne.
Ita ma Majalisar musulmin Birtaniya ta bukaci ganin tsohon ministan harkokin wajen na Birtaniya ya nemi gafara.
A cikin watannin bayan nan a nahiyar turai an tsananta muzanta suturar hijabi da matan musulmi suke sanyawa.